On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Doyin Okupe ne Mataimakin Peter Obi

A jiya ne Tsohon Kakakin shugaban kasa Dr Doyin Okupe, ya aiyana kansa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP.

Ya bayyana hakan ne a yayin  wata hira da gidan talabijin na kasa a jiya.

Idan har abunda  ya  fada  ya tabbata, shine  wanda zai yiwa  Peter Obi takarar  mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Sai dai kuma da Yuwar Dr Okupe  ya rike  matsayin a matsayin na wucin gadi, domin kaucewa  saba  wa'adin  da  Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta ta bawa jam’iyyu, na bayar da sunayen yan takarar shugaban kasa da Mataimakansu.

Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da  ta fito daga  Peter Obi ko kuma jam’iyyar  ta  LP