On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dr Ado Hamza Soron Dinki Ya Rasu

Marigayi Dr Ado Hamza Soron Dinki

Allah ya yiwa kwararren likita na farko a bangaren Kunne da Hanci da Kuma makwagoro a jihar Kano, rasuwa.

Dr Ado Hamza Soron Dinki ya rasu ne da karfe 10 da mintina 30 na daren Litinin, 14 ga watan Nuwambar 2022.

Yayi shuhura ta bangaren Likitanci a bangaren cututtukan Hanci, Kunne da Kuma makwagoro.

Ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2019, bayan ya hidimtawa mutane da basirar da Allah ya bashi.

An sallaci Gawarsa a Soron Dinki dake cikin Birnin Kano.

More from Labarai