On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dr Nasiru Idris Na Jam'iyyar APC Ya Zama Sabon Gwamna A Jihar Kebbi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Dr Nasiru Idris amatsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kebbi.

Jami’in zabe na INEC, Farfesa Sa’idu Yusuf, yace Idris ya lashe zaben ne da kuri’u dubu 409 da 225 inda  abokin karawarsa, Aminu Bande na PDP  ya samu kuri’u dubu 360 da 940 a zaben.

Farfesa Yusuf ya ce an yi wa mutane dubu 95 da 897 rijista a akwatunan da aka sake zaben yayin da aka tantance masu kada kuri’a dubu 40 da 186.

Idan za’a iya tunawa dai an fara gudanar da zaben gwamnan ne a ranar 18 ga watan Maris, amma hukumar zabe ta INEC ta ayyana cewa bai  kammala ba saboda  tashe-tashen hankula da Aringizon  kuri’u.