On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

DSS Zata Binciki Yadda Aka Baiwa Hamatta Iska Tsakanin Jami'anta Da Masu Tsaron Gidan Gyaran Hali

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi alkawarin yin bincike kan abunda ya haddasa baiwa Hamatta Iska tsakanin jami’anta da kuma jami’an tsaron gidajen gyaran hali a babbar kotun taraiyya dake Ikoyin jihar Legas, a ranar Talatar data gabata.

Idan ba’a manta ba  hatsaniya  ta barke  jim kadan bayan da kotun ta bada belin dakataccen gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele,  tare da bada umarnin cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali ,zuwa  lokacin da zai kammala cika sharuddan bada  shi beli,  to sai dai  jami’an tsaron  farin kaya  na DSS  sun sake  damke shi,  tare da  yin awon gaba dashi zuwa komarsu.

Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya  ta cikin wata sanarwa  da  ya fitar a jiya, Ya baiyana abunda ya faru a matsayin abun ban  takaici,  wanda ya  ce  hakan ba kwarewa ba ce  a yanayin gudanar da aikin nasu.

Y ace tuni  hukumar ta fara bincike kan abunda ya faru.