On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Duniyar Kwallo Na Cigaba Da Jimamin Mutuwar Pele

MARIGAYI PELE

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya dan asalin kasar Brazil Pele ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Shahararren dan wasan kwallon kafar na Brazil Pele, wanda shine dan wasa mafi girma a tarihi kuma wanda ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku ya rasu bayan yayi fama da cutar daji.

'Yarsa Kely Nascimento ce  ta sanar da mutuwar  mahaifin nasu a shafin ta  na  Instagram a  ranar   Alhamis.

Kwamitin shirya  wasannin Olympic na duniya, ya nada shi  a matsayin  gwarzon  dan wasan karni a shekarar 1999, Pele shi ne dan kwallon kafa daya tilo a tarihi da ya lashe gasar cin kofin duniya guda uku  a shekarar  1958 da shekarar  1962 da kuma shekarar  1970.

Dan wasa Pele da  ake yiwa  inkiya da Sarki, ya zira kwallaye sama da  dubu 1 da 200, kafin ya yi ritaya  daga buga tamaula a shekarar  1977.

Nan kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran  shugabannin duniya da ‘yan wasan kwallon kafa da ke aikewa da sakon ta’aziyya bisa ga  rashin  fitaccen dan wasan kwallon kafar Brazil, Pele da aka yi,  wanda ya  mutu a  ranar Alhamis yana da shekara 82 a duniya.

Shugaban kasa, Buhari ya bayyana shi a matsayin wanda duniya ba za ta taba mantawa da shi ba saboda gudunmawar da ya bayar a bangaren wasan kwallon kafa.

Marigayin yayi  fama da  cutar Koda, da  Kansar  Hanji, kuma anyi masa tiyata ta karshe a cikin watan Satumbar 2021.

Koda  a  farkon wannan makon da muke ciki, an ga Pele a cikin wani faifan bidiyo, yana yin sakon bankwana ga iyalansa da abokai da kuma sauran masoya, a yayin da jita-jitar  tsanantar rashin lafiyarsa  ta yi kamari.