On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

EFCC Na Zargin Matawalle Da Wawure Bilyan 70

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC , ta ce a yanzu haka tana kan binciken gwamnan jihar Zamfara, mai shirin barin gado, Bello Matawalle saboda zarginsa da yin awon gaba da tsabar kudi, naira da gugar naira har milyan dubu 70.

Shugaban hukumar, Abdul Rashid Bawa ne ya baiyana  haka, Ta  bakin mai magana da  yawun hukumar Osita  Nwajahat, yayin wani taron manema labarai  da aka shirya ranar Alhamis  a  Abuja.

Kazalika  shugaban hukumar  ta EFCC,  Ya  tabbatar da cewar har  yanzu suna rike da tsohon ministan lantarki Sale Mamman, wanda  jami’an hukumar  suka  cafke saboda  zarginsa  da  wawure  naira milyan dubu 22.

Bugu da kari  shugaban hukumar ta EFCC, ya  bukaci ‘yan Najeriya  da kada  su maida  hankali da kalaman  da gwamna  ya yi a kwanan nan, wanda  yake ganin baikensa  bisa  zargin cewar  ba  ya  bincikar waziran gwamnatin shugaban kasa  Muhammadu Buhari, sai dai gwamnoni.