On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

EFCC Ta Cafke Manajan Wani Banki Da Ya Boye Sabbin Kudi

EFCC

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ta cafke manajan wani banki saboda zarginsa da boye sabbin takardun kudi da aka sauyawa fasali.

Kakakin hukumar  Wilson  Uwujaren,  shine  ya  tabbbatar da haka a  ranar  Litinin,  duk da cewar bai baiyana  sunan  manajan  bankin da ake zargi  da aikata  lefin ba.

Ya  ce  an dakume  manajan  bankin ne  saboda  yadda  yaki  amincewa  a  saka sabbin takardun kudin  a cikin injinan  cirar  kudi na ATM, duk kuwa  da cewar bankin  nasa  ya samu  sabbin kudi har naira  milyan 29.

Ya  kara  da cewar, a  lokacin da suka gano an boye sabbin takardun kudin,  jami’ansu  sun tabbatar da an raba su  ga  mutanen  da suka shafe  tsawon lokacin akan layi  suna  dakon  samun kudin.

Daga  nan sai yayi kira  ga  jama’ar  kasa, dake shan  wahala  wajen samun kudinsu a bankunan da suke ajiya, kuma suke zargin a kwai  wata ‘kullalliya a ‘kasa,  da  su gaggauta   lalubar  hukumar ta EFCC  domin yin abunda  ya kamata.