On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

EFCC Ta Fara Kwato Naira Bilyan 30 Daga Hannun Dakataccen Babban Akanta Na Kasa

Dakataccen Babban Akanta Na Kasa Ahmed Idris

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa EFCC, Ta ce zuwa yanzu ta kwato naira bilyan 30 daga hannun dakataccen babban akanta na kasa, Ahmed Idris, da ake tuhuma da wawure naira bilyan 109.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya baiyana haka a ranar  Alhamis lokacin da yake jawabi, a yayin taron manema Labarai na fadar shugaban kasa, da aka shirya a fadar mulkin kasar nan dake Villa Abuja.

Bawa wanda yayi bayani kan aiyukan da hukumar ta gudanar kawo wannan lokaci a karkashin ikonsa, Ya  ce  har yanzu hukumar bata janye tuhumar naira bilyan 7 da milyan 100  da  take yiwa tsohon gwamnan jihar Abia, kuma Bulaliyar majalisar  dattawa a halin yanzu, Sanata Orji Kalu ba.

Ya ce babu kotun data sallami Sanatan ko kuma ta wanke shi daga zargin, a saboda haka har yanzu hukumar EFCC  na bin kadin al’amarin.