On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

EFCC Ta Karbi Korafin Bukatar Kama Ganduje Saboda Zargin Almundahanar Dala Milyan 5

ata kungiya mai zaman kanta, dake rajin yaki da rashin adalci, War against Injusice, Ta bukaci hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, data kama tare kuma da yin bincike sannan kuma ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje gaban kotu, saboda zarginsa da aikata almundahanar Dala Milyan Biyar.

Bayanin hakan na kunshe  ne cikin wata wasika  mai dauke dasa hannun daraktan kungiyar, Umar Ibrahim Umar, mai dauke da kwanan wata  30  ga  watan jiya,  wadda kuma  aka gabatar da ita,  ga babban jami’in  shiyyar  Kano na hukumar ta EFCC.

Umar  ya bukaci  hukumar  ta EFCC  data  dauki mataki kamar  yadda  take  binciken sauran  ‘yan Najeriya  da ake  tuhuma da aikata  irin wannan lefi.

Mai shigar da korafin ya  kuma yi kwafin  shugaban  hukumar  EFCC a  cikin wasikar  domin gaggauta  daukar  mataki a kansa.