On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Fadar Shugaban Kasa Ta CeShugaban Kasa Zai Ajiye Mulkin Kasar Cikin Amince Fiye Da Yadda Ya Same Ta

Buhari

Mashawarci na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar yada Labarai da kuma wayar da kai, Femi Adesina, Ya ce sai da ya shafe tsawon watanni takwas yana fama da rashin lafiya a shekarar 2017.

Adesina  ya baiyana haka ne a yayin wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na kasa.

A lokacin da yake karin haske  dangane da manufofi da kuma akidu na gwamnatin  shugaban kasa Muhammadu Buhari, Adesina ya  ce  shugaban kasar, sai  da  ya dauki tsawon watanni takwas yana ganin likita a kasar Burtaniya a shekarar  2017.

Sai dai ya  ce  duk da wannan kalubale da aka fuskanta,  Shugaban kasar  zai ajiye mulkin Najeriya cikin salama da kuma  samun  dimbin cigaba.

Mai magana da yawun shugaban kasar,Ya  ce  a lokacin da Buhari  ya karbi mulkin kasar nan,Kananan hukumomi 17 ne suke a hannun  mayakan  tada kayar baya a shekarar 2015,  Sai dai kuma a halin yanzu  gwamnati  ta samu gabala akan mayakan  na tada kayar  baya.