On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Farashin Naman Shanu Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

NAMAN SHANU

Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin kayan abinci kamar naman sa da shinkafa sai wake da albasa da Doya da sauransu sun karu a watan Satumbar bana.

Rahoton ya ce matsakaicin farashin tsokar naman sa mai nauyin kilo daya  ya karu da kaso 28 da digo 8 daga  kan naira dubu 2  da 199 da ake siyar dashi a cikin watan  Satumban bara  zuwa Naira dubu 2 da 816 da kobo 91 a watan Satumban bana.

A binciken da aka gudanar kan jihohin da aka fi samun tsadar naman sa, Ya nuna  cewar  Jihar Anambara ana siyar da kowanne kilo daya akan naira  dubu 3 da 800, Yayin da jihar Kogi  ta fi kowacce jiha saukin yadda ake siyar da naman akan naira dubu 1 da 845 kan kowane  kilo daya.

A yankin Kudu-maso-gabashin kasar nan  kuwa, an fi samun tashin farashin shinkafa a yayin da   yankin arewa ta tsakiya aka fi samun saukin farashin shinkafar a cikin watan satumbar bana, kamar yadda hukumar kididdiga  ta kasa NBS ta baiyana.