On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Farfesa Soyinka Ya Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Kungiyar Fulani Ta MACBAN Kamar Yadda Ta Haramta IPOP

Fitaccen masanin adabin turanci farfesa Wole Soyinka ya bukaci gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar Fulani makiyaya ta miyatti Allah da akafi sani da MACBAN amatsayin haramtacciya.

A lokacin  da  yake  tattaunawa  da  gidan  talabijin  na  channels  a  daren  ranar talata,  Wole  Soyinka  ya  baiyana  rashin gamsuwa akan yadda  gwamnatin  tarayya  ke shawo  kan   rikicin  manona  da  makiyya  a  fadin  Najeriya.

Daga  nan  ya  bukaci  gwamnatin  tarayya  ta haramta  kungiyar  miyetti  Allah kamar  yadda  ta  haram kungiyar  masu  fafutukar  kafa  kasar  Biafra IPOB  saboda  yunkurin  ballewa  daga  yankin  kudu  maso  Gabas  daga  Najeriya 

Soyinka ya dage kan cewa dole ne Najeriya ta yi la'akari da tarihinta, ta yadda za ta fuskanci kalubalen tsaro.