On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Fargabar Fuskantar Fari Ta Tilastawa Manoman Jihar Borno A Najeriya Shirya Addu'ar Rokon Ruwa

Yayinda damunar bana kecigaba da kankama manoma a birnin Maiduguri na jihar Borno na shirye-shiryen gudanar da addu'o'i na musamman kan jinkirin saukar ruwan sama a jihar  dake arewa maso gabashin Najeriya.

Al’amarin ya shafi manoma da galibinsu suka fito daga  yankunan arewaci da tsakiyar jihar, inda suka ce suna son a hada kai ne domin neman taimakon Allah kan matsalar.

Daya daga cikin manoman mai suna Ibrahim Ali ya koka da yadda suke ganin hadari  kamar za a yi ruwan sama amma bayan wani lokaci sai ayi iska mai karfi  hadarin ya washe.

Majalisar masarautar Borno, tace tana goyon bayan addu’o’in.

A wata sanarwa da ta fitar, Majalisar tace ta hada kan jama’a domin gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama na musamman da aka shirya gudanarwa a yau Litinin 17 ga watan Yuli 2023 a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.