On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Fernando Santos Yayi Murabus Daga Horas Da Tawagar Kasar Portugal

SANTOS

Fernando Santos ya yi murabus daga matsayinsa na mai horas da tawagar Portugal a ranar Alhamis bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Morocco a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya.

Hukumar kwallon kafar PortugaF ta ce an cimma yarjejeniya da Santos mai shekaru 68 da haihuwa  domin kawo  karshen aikin horaswar da yake yiwa kungiyar, wanda ya fara tun daga shekarar 2014.

Hukumar ta kuma yaba masa game da irin gudunmuwar da ya bayar ta bangaren ganin kungiyar ta samu nasara a matakai daban daban.