On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Firiyiministan Kasar Italiya Yayi Murabus.

Draghi

Firayim Ministan Italiya Mario Draghi ya yi murabus daga mukaminsa bayan da kawancen jam’iyyun ‘yan biyar a kasar suka janye da goyon bayansa a wata kuri'ar nuna kwarin gwiwa da aka kada.

Sai dai shugaban kasar, Sergio Mattarella ya ki amincewa da murabus din, inda ya  ya buka ce  shi  da yayi  jawabi ga majalisar dokokin kasar domin ba da cikakken bayani akan halin da siyasar kasar ke ciki.

Ana saran Mr Draghi zai je majalisar dokokin kasar  a ranar Laraba mai zuwa, bisa hasashen cewa zai iya cigaba da zama akan kujerarsa, sakamakon shiga tsakanin  da shugaban kasar Mattarella yayi.