On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ganduje Na Fuskantar Cikas Daga 'Yan Kwamitin Gudanarwa A Yunkurin Zama Shugaban Jam'iyyar APC

Wasu alamu sun bayyana cewa wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa na iya samun takaddama da gwamnonin jam’iyyar kan shirin gwamnonin na daukar tsohon gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Hakan dai ya biyo bayan murabus din da Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore suka yi a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar na kasa bisa zargin karkatar da kudade.

Sa’o’i kadan bayan labarin zaben Ganduje ya bazu, an samu rarrabuwar kawuna tsakanin jiga-jigan jam’iyyar da ‘yan jam’iyyar kwamitin gudanarwa kan shirin nada tsohon gwamnan Kano mai shekaru 73 a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wasu ‘yan jam’iyyar APC na kwamitin gudanarwa sun shaidawa jaridar PUNCH cewa suna adawa da shirin gwamnonin, inda suka dage cewa an ware gurbin ga yankin Arewa ta Tsakiya, kuma Ganduje ya fito ne daga shiyyar Arewa maso Yamma.