On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ganduje Ya Amince Da Sakin Kudi Naira Milliyan 300 Domin Biyan Kudin Makaranta Ga 'Daliban Kano A Kasar Cyprus

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sakin naira miliyan dari uku a matsayin kudin makaranta ga daliban Kano dake karatu a jami’ar Near East a kasar Cyprus.

Kwamishiniyar ilimi mai zurfi Dr Mariya Mahmoud Bunkure itace ta bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Sunusi Abdullahi Kofar Na’isa ya fitar.

Bunkure ta ce biyan kudin ya kasance cika alkawarin da Gwamnan ya yi na daga likafar zamantakewar al’umma da bunkasa  matasan jihar Kano ta hanyar samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.

More from Labarai