On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ganduje Ya Ce Jahar Kano Zata Baiwa Tinubu Kuri'ar Data Fi Kowace Jaha Yawa

TINUBU DA GANDUJE

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar Legas da su marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima baya a zaben shekarar 2023.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin wata ziyara da Shettima, da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas,  suka kai wa al’ummar Arewa mazauna Alaba Rago a yankin Ojo na jihar ta legas.

Ya ce tuni yankin arewacin kasar nan ya riga ya karbi tsarin Bola Tinubu a matsayin dan takara.

Ya kuma ba da tabbacin cewa Asiwaju zai samu kuri’u a Kano fiye da yadda kowace jiha za ta ba shi.