On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ganduje Ya Ce NDC Ba Za Ta Lashe A Kano Ba

Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NDC ba zai yi nasara a Jihar Kano ba a zaɓen shekarar 2027.

Da yake zantawa da manema labarai jiya, Ganduje ya ce tikitin haɗin gwiwar ba shi da ƙarfin siyasa da tarihin shugabancin da zai iya jawo goyon bayan al'ummar Kano.

Ya kuma ce tarihin mulkin Peter Obi a matsayin gwamnan Jihar Anambra bai nuna yana da ƙwarewar da ake buƙata wajen jagorantar Najeriya ba.

Ganduje ya kuma soki tarihin siyasar Kwankwaso a Kano, yana mai cewa bai samu damar yin wa'adi biyu a jere a matsayin gwamnan jihar ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C