On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ganduje Ya Dakatar Da Bikin Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni Saboda Aftila'in Kasuwar Beruit

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin da aka shirya gudanarwa yau domin alhini kan wadanda suka makale sanadiyar rushewar bene mai hawa uku  a kasuwar Beirut

 

Da yake jajantawa wadanda iftila'in ya shafa, gwamna a  wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayar da umarnin a kara kaimi wajen  aikin ceto wadanda suka makale a cikin baraguzan ginin.

Yayin da yake bayyana damuwa  akan al'amarin, ya bayar da tabbacin cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.

Sanarwar ta kuma jajantawa  wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a ranar Litinin da ta gabata a sassa da dama na jihar Kano, inda aka yi asarar dukiya  mai yawa sanadiyar mamakon ruwan sama.