On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ganduje Ya Koka Kan Hana Ma'aikata Dubu 10 Da Ya Dauka Aiki Albashi

GANDUJE DA ABBA GIDA-GIDA

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da ya dauka aiki, da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi.

Tsohon gwamnan  ya koka ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar kano, Muhammad Garba  ya fitar a ranar  Laraba, a wani bangare  na goron barka da babbar Sallah.

Ganduje  ya  ce  dakatar  da biyan albashin ma’aikatan da  ya dauka aiki  ya haifar da firgici a zukatan ma’aikatan kano, a  lokacin da  jama’a  ke fadi tashin yadda  zasu tsira da  rayuwarsu.

Kazalika  tsohon gwamnan jihar Kanon,  ya nuna damuwarsa  kan soke  karin girma da kuma na matakin albashi da ya yiwa malaman makarantun firamare,  da gwamnan kano mai  ci  ya  yi.