On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ganduje Ya Rushe Majalissar Zartaswa Ta Gwamnatin Kano

“Kuna da sauran wa’adi daga yanzu  zuwa ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu da muke ciki na  2023, ku  mika al'amuran hukumomin ku ga manyan sakatarori  ko Daraktocin mulki da kudi.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ke bada wannan umarni ga dukkan masu rike da mukaman siyasa a jiharnan gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce wadanda abun ya shafa  sun hada da kwamishinoni da  masu ba da shawara na musamman, da manyan jami’an gudanarwa na kamfanoni mallakar gwamnati da dai sauransu.

Sanarwar ta kuma ce jami’an gwamnati da aka nada a hukumomi  wadanda keda dokoki kan takamaiman lokaci su ne kawai zasu cigaba da aiki.