On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ganduje Ya Soke Izinin Mallakar Filin Da Ginin Bene Ya Rushe A Kasuwar Beruit Tare Da Maida Wurin Filin Ajiye Ababen Hawa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kwace Izinin mallakar filin ginin nan mai hawa uku da ya rushe a kasuwar wayoyin sailula ta Beirut.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar, Ganduje yace  “tunda farko ya kamata wurin ya zama filin ajiye ababen hawa kawai, kuma  ya yi kankanta da gina shaguna. 

Yayin  ziyarar da ya kai wurin da al'amarin ya faru, gwamnan ya tunatar da cewa, an kafa wani kwamitin kwararru mai karfi da zai binciki musabbabin aukuwar lamarin. 

"Ya kamata mu sani cewa, daga farko duk wani gini ya kamata a tsara shi tare da kulawar  kwararru, inji Ganduje.

Acewar  gwamnan na Kano, cikin mako guda  kwamitin zai gabatar da rahotonsa, kuma za'ayi aiki da rahoton yadda ya kamata"

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su baiwa ma’aikatan da ke aikin tono ceti hadin kai, inda ya kara da cewa, bayan an kammala  gwamnati za ta fara samar da filin ajiye ababen hawa.
...