On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ganduje Ya Yi Alkawarin Farfado Da Jam'iyyar APC

GANDUJE

Nan kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin farfado da martabar jam’iyyar APC.

Ganduje ya baiyana haka ne a Abuja lokacin da yake karbar  bakuncin  wata  kungiyar masu goyon bayan jam’iyyar APC ta kasa,gabanin sanar dashi a matsayin shugaban jam’iyyar  na kasa a hukumance.

Kazalika  ya baiyana takaicinsa  dangane da  Murabus din  da Salihu Lukman  ya yi  daga kan matsayin mataimakin  shugaban jam’iyyar  na kasa mai kula da shiyayr Arewa  maso yamma.

A cewarsa  bai kamata  ya sauka  daga kan kujerar  ba, kasancewar  yana  fadar  ra’ayinsa ne   ga jama’a, kan kalubalantar dora Gandujen a matsayin  shugaban jam’iyyar na  kasa.