On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Daukar Hayar Kungiya Domin Bata Sunan Tsohuwar Gwamnati

Gwamnatin da ta shude a jihar Kano ta bayyana wani labari amatsayin yaudara da rashin gaskiya da ke nuna cewa ta samu lamuni na Naira biliyan 10 domin samar da Kyamarorin tsaro CCTV a cikin birnin jihar.

A wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ya fitar, ya ce an dauki hayar  wata kungiyar hadin gwiwa dake nazarin harkokin siyasa da gwamnatin domin bata sunan tsohuwar gwamnati ta hanyar Ikirari akan kudaden.

Garba ya bayyana cewa da gaske gwamnatin da ta shude ta kudiri aniyar  aikin  domin inganta harkar tsaro a jihar, amma wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar 1 ga Yuli na  2022 ta bayar da umarnin hana gwamnati karbar lamunin.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 37°C | Low: 23°C