On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gara Ta Cinye Wasu Muhimman Takardun Yadda Aka Kashe Sama Da Naira Bilyan 17 A Hukumar Inshorar Al'umma Ta Kasa

HOTON GARA

Ana zargin Gara ta cinye wasu muhimman takardu asusun amintattu na Hukumar Inshorar Al’umma ta kasa, masu dauke da bayanan yadda aka kashe zunzurutun wasu kudade har naira bilyan 17 da milyan 100, kamar yadda jami’an hukumar suka baiyanawa majalisar dattawa.

Jami’an  Hukumar  sun  baiyana haka ne  a  lokacin da suka baiyana gaban kwamitin majalisar dattawa  mai kula da baitul  malin gwamnati.

Bayanin hakan dama  sauran wasu jawabai na kunshe ne cikin wani rahoton babban mai kididdiga na kasa  da aka fitar tun a shekarar  2018.

INSHORA  22

Binciken ya biyo bayan yadda  Babban Mai kididdiga na kasa  ya tuhumi hukumar  asusun amintattun Inshora ta kasa,  kan yadda  ta kashe wasu kudade  tun daga shekarar   2018.