On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Garba Shehu Ya Mayarwa Da Tinubu Martani

BUHARI DA TINUBU

Kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, Ya ce da mai gidansa ya cire tallafin man fetir, Da shugaban kasa na yanzu, Bola Tinubu ya fadi a zaben shugaban kasa.

Idan ba’a manta ba, Shugaban kasa mai ci, a  lokacin da yake jawabi ga wasu  ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa,  Ya ce  rashin kwarin gwiwa ce  ta  sa  aka ki  janye tallafin man,  kafin  shi  ya kaiga  daukar matakin cire shi  baki daya, a lokacin da  ya gabatar da jawabi ga ‘yan kasa, jim kadan bayan  shan rantsuwar kama aiki.

Sai dai a wata sanarwa  da  kakakin tsohon shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar a  ranar Litinin, Ya kare matakin da  tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na kin janye  tallafin man fetir,  domin gudun kada  jam’iyyar APC  ta  sha kaye  a zaben shugaban kasa a da aka yi ranar  25 ga watan fabarairun bana.

Garba Shehu  ya  ce , Kamata  ya yi  Tinubu ya zama dan siyasa mai  gaskiya, sannan kuma ya  gane cewar  da  an janye  tallafin man, ta hanyar aiki da dokar  sarrafa albarkatun man fetir, to babu shakka da jam’iyyarsu  ta fadi a zaben da  ya  gabata.