Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta yi babban abin mamaki bayan ta farfado daga ci 2-0 da Masar ke yi mata, ta kuma yi nasara da ci 3-2 domin tsallakawa zuwa zagayen ukun karshe tare da cigaba da raya burin Lionel Messi, na sake lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya.
Masu riƙe da kambun gasar sun kusa yin bankwana da ita bayan da Yasser Ibrahim da Mostafa Ziko suka ci wa Masar ƙwallaye biyu, yayin da Messi ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaran raga.
Sai dai Cristian Romero ya fara dawo da Argentina cikin wasan bayan da ci wata kwallo ta hanyar dasa mata kai, yayinda ƙungiyar ta zura ƙwallaye uku cikin mintuna 11 na ƙarshe da kuma lokacin da alƙali ya ƙara.
Messi ne ya ci ƙwallon da ta dawo da wasan kunnen doki, wanda hakan ya kai adadin kwallaye da ya zura a raga a gasar zuwa 9, tare da komawa kan gaba a jerin wadanda ka iya lashe kambun takalmin zinare da ake bawa dan wasan da ya fi kowa jefa kwallaye a raga a gasar.
Daga bisani Enzo Fernández ya tabbatar da nasarar Argentina a minti na biyu na ƙarin lokaci.
Bayan tashi daga wasan, an ga Messi na zubar da hawaye na farin ciki yayin da yake rungumar abokan wasansa bayan nasarar da suka samu.
A ɓangaren Masar kuwa, 'yan wasan da jami'an ƙungiyar sun nuna rashin jin daɗinsu kan wasu hukunce-hukuncen alƙali da suka ce sun cutar da su, ciki har da ƙin amincewa da wata ƙwallo da suka ci a farkon zagaye na biyun wasan, yayin da aka kuma bai wa ɗaya daga cikin jami'an masu horas da su jan kati bayan ƙwallon da Argentina ta ci ta nasara.
Comments
Add a comment