On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gasar Cin Kofin Duniya ta Shekarar 2022, Rana ta 5

Ana cigaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022, wacce kasar Qatar ke karbar bakunci. A jerin wasannin da aka buga jiya, ‘kasar Ghana, ta zamo kasa ta farko daga nahiyar Afrika da ta samu damar jefa kwallo a raga a gasar ta bana. Sai dai wannan dama bata hana kungiyar shan ruwa a hannun Portugal ba da ci 2 da 3.

Yayin wannan wasa, dan wasa Christiano Ronaldo ya sake kafa sabon tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya jefa kwallaye a rage a gasar cin kofin duniya daban-daban sau 5 a jere. Christiano Ronaldo ya leka ragar ne ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga da kungiyar ta sa ta samu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 65.

Murna ta koma ciki wa kungiyar Portugal bayan da ‘dan wasa Andre Ayew ya farke kwallon Ronaldo a minti na 73, wanda ya bude ruwan kwallaye da aka sha daga baya a wasan da ya ja hankali matuka. A minti na 78 ne ‘dan wasa Jao Felix ya sake tura Portugal gaba.

Rafael Leão  ya kara wata kimanin mintina 10 a tashi, sai dai dan wasa Usman Bakari ya sake rage wannan tazara a minti na 89.

A daren jiyan ne har ila yau, Brazil wacce ke naman sake lashe gasar bayan farin da ta sha fama da shi tsahon shekaru 20 da suka gabata, ta buga wasan ta na farko a gasar ta bana, inda ta yi wa Serbia shakar mutuwa da ci 2 da 0. ‘Dan wasan gaba mai wakiltar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, Richarlison ne ya jefa tagwayen kwallayen a raga domin tabbatar da cewa kungiyar ta fara gasar da kafar dama.

Sauran wasanni da aka buga sun hadar da, Uruguay da kasar Koriya, wanda aka tashi kowacce kungiya na nema sai wasan da Switzerland ta doke Ghana da ci 1 tak mai ban haushi ta hannun dan wasa Breel Embolo.

A wasan farko na Juma’a, Iran ce ta yi Karin kumallo da kasar Wales da ci 2 da 0. ‘Yan wasa Ramin Rezaeian  da Roozbeh Cheshmi ne suka jefa kwallaye a raga domin tabbatar da nasarar kasar. Sauran wasanni da za’a buga a yau sun hadar da wasa tsakanin mai masaukin baki, Qatar da kuma kasar Senegal.

Daga bisani, Netherlands zata kece raini da Equador kafin a buga wasan karshe na yau tsakanin Amurka da kasar Ingila.

Ku kasance da Arewa Radio domin jin yadda zata kaya kai tsaye a wadannan wasanni, kuna kuma da damar samun tukuici idan kuka yi hasashen yadda sakamakon wasan zai kasance. Ku mana comment da hasashen ku a kasa, ku kuma hada da lambar wayoyi. Za mu dauki mutun na farko da yayi hasashen daidai.