On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gawuna Ya Yiwa Abba Gida-Gida Addu'ar Fatan Alkhairi

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi Addu'ar fatan Alkhairi ga Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP bisa nasarar da ya samu zaben gwamna na 2023

A cikin wani sakon murya da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikewa manema labarai a yau, Gawuna ya tunatar da magoya bayan sa cewa  Allah ne ke bayar da mulki kuma yana bayarwa ga  ga wanda ya so. 
A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC ta rubuta ƙorafe-ƙorafe kan cewa a yi duba a sakamakon zaɓen domin akwai kura-kurai.
Ya kara da cewa duk da wannan yunkuri da APC ta yi na a sake tantance sakamakon zaɓen tare da sake zabuka a wasu gurare, sai INEC ɗin ta baiwa Abba shaidar lashe zabe a yau Laraba.
Gawuna y ace, “Sabo da haka, tunda hukumar zaɓe ta daɗa tabbatarwa da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP zaɓen a yau 29 ga watan Maris, to ina mai tunawa magoya bayan mu cewa tun a baya mun yi addu’a cewa in alheri ne, Allah Ya bamu, in kuma babu alkhairi, Allah Ya canja mana da abinda ya fi alkhairi.
“Shi kuma wanda ya ci zaɓen, muna masa addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba na gari.
Har ila yau Gawuna ya yi addu’a Allah ya sa mu zama masu biyayya ga shugabanci da kuma bin doka. Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya.