On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gidaje 250 Ne Suka Salwanta Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Jihar Sokoto

AMBALIYAR RUWA

Ambaliyar ta lalata gidaje kimanin 250 a wasu garuruwa dake cikin karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Kakakin Hukumar Bada agajin gaggawa na jihar, Abubakar Ghani shine ya  ya tabbatar da haka  ta cikin wata sanarwa, yana mai cewa  mutane da dama ne suka  rasa muhallansu.

Ya kara da cewa  abun alhinin ya faru ne a karshen mako, inda amaliyar ta shafi garuruwan da suka hada da Shiyar Ajiya da kuma Runji.

Mashawarci  na musamman ga gwamnan jihar Aminu Waziri  Tambuwal , Alhaji  Zubairu  Magaji wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa  garuruwan, Yace  gidaje 250 ne suka  lalace a garuruwa  ukku.