On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Girman Zunubin Buhari Ya Fi Karfin A Yafe Masa Inji IPOB

BUHARI

kungiyar nan ta ‘Yan awaren yankin kudu maso gabashin kasar nan da aka fi sani da IPOB, ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, Inda ta baiyana cewar girman zunubin da ya aikatawa ‘yan Najeriya abune da ba za’a taba yafe shi ba.

Ta cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar  Emma Powerful  ya fitar,  Kungiyar  ta maida martani ne kan   neman yafiya  da shugaban kasar ya  yi  ga  wadanda  ya  bata mawa  saboda  yanayi na  gabatar  da aiki, a  kwanan nan.

Sanarwar da  kungiyar ta  Fitar,  Ta  ce  zunubin da  shugaban kasar ya aikata  abune  da  ba za’a yafe  ba,Kuma zai girbi abunda  ya aikata  a lokacin da  ya kammala mulki.