On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gobara Ta Kone Dakunan Karatu A Wata Makarantar Kwana Ta Tsangaya A Kano

Wata gobara ta kone ajujuwa 14, wani rukunin ajujuwa da bandakuna a makarantar kwana ta Tsangaya dake kauyen Kiyawa a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a Kano, ya ce al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.

Abdullahi ya ci gaba da cewa, gobarar ta kone wani gini a makarantar ta Tsangaya dauke da ajujuwa 14, da ofisoshi 12 na bangaren gudanarwa da kuma bandakuna 21 gaba daya.

Ya ce gobarar ta tashi ne daga na’urar lantarki mai amfani da  hasken rana a babban zauren bangaren  gudanarwa.

A wani bangaren kuwa, hukumar tace a ranar Asabar ta samu kiran gobara daga Ladanai Tsamiya titin Babba inda wani kango da ake amfani da shi amatsayin wurin sarrafa ba’kin mai ya kama da wuta.

Black oil 1

Saminu Yusif Abdullahi yace akwai lita dubu 7 zuwa dubu 8 ta bakin man a depo din wanda jami’an hukumar sukayi nasarar ceto 75 na bakin man.

Yace har yanzu akan kam gudanar da binciken musabbabin gobarar.

black oil 2