On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamantin Taraiyya Tace Ya Zama Tilas Tayi Karin Haraji Akan Kudin Kira Da Kuma Data

MINISTAR kUDI ZAINAB SHAMSUNA

Duk da tarin sukar da ake samu daga bangaren masu ruwa da tsaki da kuma masu amfani da Kayayyaki, gwamnatin taraiyya tace ba gudu ko ja da baya kan shirinta, na kara harajin kudin kiran waya da kuma na amfani da Data da kimanin Kaso 5 bisa 100

Da zarar an  fara aiki da sabon tsarin, yan Najeriya  zasu rika biyan  kaso 12 da digo  5 bisa 100  akan kiran waya da kuma  kaso  7 da digo 5 bisa  100 .

Ta cikin wata sanarwa da Kakakin Ministar  Kudi  Zainab Ahmed Shamsuna, Tanko Yunusa , Yace kaso biyar bisa 100 na harajin zai rika shiga ne aljihun gwamnati.

Kazalika ministar tace  sanarwar dake yawo  kan harajin tuni aka aike da ita ga ministan sadarwa na kasa da sauean hukumomin da abun ya shafe.