On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamna Abba Na Jihar Kano Ya Dora Kwamishinoninsa A Matakin Gwaji Na Wata 6

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, ya sanya sabbin kwamishinonin da aka rantsar a matakin gwaji na tsawon watanni shida, daga nan kuma za a tantance gwazonsu bisa la’akari da yadda suke gudanar da ayyukansu.

Gwamnan ya ce idan aka tantance kwamishinonin da sukayi kwazo za a yaba musu sannan kuma za a sallami wadanda suka gaza.

Ya bayyana haka ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jiha da ya jagoranta a gidan gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Hisham Habib ya fitar, an ruwaito gwamnan na cewa zai jagoranci tawagar sa ido da tantance ayyukan kwamishinonin da ma’aikatun su.