On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamna Abba Na Jihar Kano Ya Sake Nada Masu Bada Shawara Na Musamman

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin mutane 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman kan fannoni daban-daban.

Wadanda aka nada sun hada da Hon. Isyaku Ali Danja, mai ba da shawara na musamman kan harkokin majalisan da Hon. Muhammad Jamu Yusuf, mai ba da shawara na musamman kan hulda da jama'a na kasa da kasa da kuma Col. Abubakar Usman Garin Malam mai ritaya Mashawarci na Musamman kan kare Iftila’oi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Sanarwar ta ce sauran  sun hada da Malam Usamatu Salga, mai ba da shawara na musamman kan harkokin addinai da Hon. Abduljabbar Muhammad Umar , mai ba da shawara na musamman kan harkokin zuba jari da hadin gwiwar bangarori masu zaman kansu da Hon. Aminu Abba Ibrahim, mai ba da shawara na musamman kan ma'adanai  da kuma Injiniya Nura Hussain, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasuwanci.