On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Abba Ya Gabatarwa Majalissa Sabbin Nade-Nade A Hukumar Zabe KANSIEC

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya mika jerin sunayen mutane takwas da zai nada a matsayin mambobin gudanarwa na  hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Kakakin majalisar, Alhaji Ismail Falgore, ya karanta wasikar Yusuf a zaman majalisar a ranar Talata a Kano, ya kuma umarci wadanda aka nada su bayyana a gaban ‘yan majalisar domin tantance su a ranar Alhamis.

Hakazalika, gwamnan ya kuma gabatar da jerin sunayen karin masu bada shawara na musamman guda 10  ga  majalisar  domin tabbatar da su.

Falgore ya mika jerin sunayen ga kwamitin majalisar kan al’amuran zabe.

A wani bangaren, kwamitin majalisar kan kasafin kudi ya  mika rahotonsa kan kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar.