On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Abba Ya Nada Sabbin Mukamai 14 A Hukumomi Da Ma'aikatu

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Dr. Farouq Kurawa amatsayin manajan darakta na hukumar bunkasa aikin gona da raya karkara ta jihar Kano KNARDA.

Babban Sakataren yada labarai na gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Laraba, ya ce gwamnan ya kuma nada wasu sauran mutane 13 mukamaidaban-daban na hukumomi da ma’aikatu.

Cikin sauran mutanen akwai Jarumin fina-finai Abba El-mustapha, amatsayin shugaban hukumar tace fina-finai da ‘Dab’I ta jihar Kano sai Engr. Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na hukumar KHEDCO sai Alhaji Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari da Kaddarori na Jihar Kano KSIP, da Dokta Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da kayan Noma na Kano KASCO.

Sauran sune Hon. Sadiq Kura Muhammad, manajan darakta na gidan Zoo da Injiniya Sani Bala, manajan daraktan hukumar lantarki a karkara sai Hon. Shamwilu Gezawa, Hukumar Samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta Jihar Kano RUWASA da Alhaji Tukur Bala Sagagi, Manajan Darakta na kukumar kula da yawon bude idanu ta Jihar Kano da kuma Alhaji Yahaya Muhammad Idris manajan darakta na madaba’ar jihar Kano inda Hon. Adamu Yahaya, zai kasance mataimakin manajan darakta.

Har ila yau akwai Dr. Muhammad S. Khalil, sakataren zartaswa na hukumar magance zaizayar kasa da kula da sauyin yanayi  ta Jihar Kano KN-WECCMA da Dokta Dahir M. Hashim, Jami’in hukumar ta WECCMA a Kano.

Sanarwar ta ce nadin mukaman  ya fara aiki nan take.