On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Abba Ya Nada Sakataren Gwamnati Na Riko A Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci shugaban ma'aikata Abdullahi Musa, ya karbi ragamar ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano amatsayin rikon kwarya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a safiyar yau.

Sanarwar ta ce nadin ya biyo bayan hutun jinya da Sakataren gwamnati Dr. Abdullahi Baffa Bichi ke yi a kasar Saudiyya.

A wata Wasika daga shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Kano Hon. Shehu Wada Sagagi, ya ce shugaban ma’aikatan zai sanya ido kan harkokin offishin sakataren gwamnati har sai Dr Baffa Bichi ya dawo nan da ‘yan makonni masu zuwa.