On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Douye Diri Na Bayelsa Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar A Jam'iyyar PDP

Gwamna Douye Diri Na Bayelsa

Gwamnan jihar Bayelsa , Sanata Douye Diri ya zama dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da za’a yi ranar 11 ga watan Nuwambar bana.

An gudanar da zaben fidda  gwanin ne  a  ranar  Laraba, Kuma ba ‘a samu  wanda  ya tsaya  neman tikitin takarar  tare da  gwamnan mai ci ba

Shugaban  kwamitin shirya  zaben wanda kuma shine gwamnan jihar Osun, Sanata  Ademola  Adeleke  ya  baiyana cewar  gwamnan ya samu kuri’a  305, wanda  hakan ya bashi damar zama  dan takara  batare  da hamaiyya  ba.

Shima a nasa  jawabin, Gwamna  Diri  ya baiyana godiyarsa  ga wakilan jam’iyyar  saboda  damar da suka  sake  bashi  domin ganin ya sake yin tazarce akan kujerar  gwamnan jihar.