On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna El-Rufa'i Zai Rushe Wasu Kanfanoni 9 Mallakin Tsohon Gwamna Ahmed Makarfi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, Ya soke shaidar takardar mallakar fili ta wasu kanfanoni guda tara, mallakin tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.

Kazalika  gwamnan  ya  bada umarnin rushe  wuraren da abun ya  shafa,kamar  yadda aka aike  da takardar  sanarwa  ga  ma’aikatan dake aiki a  kanfanonin,jim kadan bayan da gwamnan jihar  ya  janye  shaidar  takardar  mallakar  fili  ta kanfanonin.

Biyar  daga cikin filayen  suna  a yankin Mogadishu  sai  guda ukku dake  akan  titin  Kwato  da  kuma wani  guda daya  a  yankin Doka.

Sanata  Makarfi wanda  ya  tabbatar da daukar  matakin ga manema Labarai a ranar  Alhamis, Yayi alkawarin cewar  lauyansa  zai garzaya  gaban kotu  domin hana daukar matakin rushe  wuraren.