On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Ya Dawo Da Rawanin Sarkin Birnin 'Yandoto

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da rawani Alhaji Aliyu Garba Marafa a matsayin Sarkin Birnin ‘Yandoto.

Idan za’a iya tunawa a cikin watan Yuli na shekarar 2022, Matawalle ya dakatar da sarkin saboda ya bada mukamin sarauta ga wani  sarkin 'yan fashi, Ado Aleiru.

Sai dai wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar a karshen mako ta sanar da mayar da sarkin kan mukaminsa.

Sanarwar ta ce mayar da Marafa bakin aiki ya biyo bayan shawarwarin kwamitin da aka kafa domin binciken al’amarin domin kwamitin bai samu wata hujja ta wata manufa ko hadin gwiwa tsakanin Sarkin da ‘yan fashin daji ba.