On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Ya Karbi ‘Yan Mata 5 Da Suka Kubuta Daga ‘Yan Bindiga Bayan Watanni 7

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya karbi ‘yan mata biyar da suka kasance ‘ya ‘yan tsohon Akanta-Janar na jihar Zamfara, wadanda aka yi garkuwa da su tsahon watanni bakwai.

Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 10, Bello Sani-Deljan shine ya gabatar da yaran ga  gwamnan a ranar Litinin, bayan kubuta daga  ‘yan bindiga da suka sace ‘yan matan biyar daga gidansu da ke karamar hukumar Bungudu a watan Maris.

‘Yan fashin dajin sun fitar da wani faifan bidiyo a watan Octoba da ke nuna ‘yan matan dauke da manyan bindigogi tare da yi musu barazanar shigar da su cikin ‘yan ta’adda idan har ba a biya kudin fansa da suka nema ba.

Gwamna Matawalle ya yabawa jami’an tsaro da suka yi nasarar ceto ‘yan matan ba tare da wata matsala ba, ya kuma bukace su da su kawo karshen masu aikata ta’adanci a jihar.

More from Labarai