On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Matawalle Ya Kafa Kwamitin Mika Mulki Cikin Lumana A Jihar Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kaddamar da kwamitin mika mulki mai mutum 41 da zai yi aikin mika mulki cikin lumana zuwa ga zababben gwamna mai jiran gado Dr Dauda Lawal Dare.

Sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe ne ya bayyana haka a birnin Gusau a ranar Alhamis, yace  kwamitin ya kunshi tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda a matsayin shugaba.

Dr Lawal Hussein, Babban Sakatare, Harkokin Majalisar Dokoki a ofishin gwamna zai kasance  a matsayin Sakatare.

Balarabe ya nunar da cewa kwamitin yana da alhakin tabbatar da mika mulki ga zababben gwamna, Dr Dauda Lawal.