On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Gwamna Matawalle Ya Kori Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Daga Jihar Zamfara

Gwamnatin jihar  Zamfara  ta  umarci daukacin kungiyoyi  masu  zaman kansu dake  aiki a  jihar  ba bisa  doka  ba, dasu  gaggauta  ficewa  daga  jihar  batare  da  bata wani lokaci ba.

Wata sanarwa  da  kwamishinan tsaro  na  jihar, Mamman  Tsafe  ya  fitar,  ta  baiyana  cewa an gano wasu  daga cikin  kungiyoyin suna temakawa  waje  matsalar  tsaro  da jihar  ke ciki  da  kuma makotanta.

Tsafe   ya  ce  an  umarci  dukkanin   hukumomi da kuma ma’aikatun gwamnati  dasu  yanke  duk  wata  alaka tsakaninsu  da kowace  irin  kungiya  batare da  wata jan kafa  ba.

Bugu da kari  ya  ce  za’a dauki matakin  hukunta  duk wata  hukuma ko ma’aikata da aka  samu  tana hulda  da irin wadannan  kungiyoyi.