On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Ortom Na Benue Ya Baiwa Makiyaya Wa'adin Makwanni Biyu Su Fice Daga Jihar

SAMUEL ORTOM

Gwamnan jihar Benue, Samule Ortom ya dakatar da gudanar da aiyukan Hukumar kula da kungiyoyin tsaro masu damara na jihar har nan da tsawon makwanni biyu masu zuwa.

Hukumar dai ita  ce wadda aka dorawa  alhakin tabbatar da dokar  nan  ta haramta yin kiwo a  fili,  Gwamnan  ya  ce  matakin  zai baiwa  makiyaya dake da dabbobi  damar  ficewa  daga cikin jihar.

Gwamnan ya baiyana daukar  matakin nea   yayin wani taro  na majalisar  tsaro  na jihar  da aka gudanar a ranar  Talata,  bayan da aka  halaka mutane  sama da 130 a cikin mako daya  a jihar.

Samuel  Ortom ya  ce  daukar  matakin zai baiwa  makiyayan da suka shiga  jihar  batare da sanin an haramta  yin  kiwo  a fili  ba,  damar gaggauta ficewa  daga cikin.