On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Rotimi Ya Dawo Najeriya Bayan Jinyar Watanni 3 A Jamus

ROTIMI

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.

Gwamnan ya bar Najeriya watanni  ukku  da suka gabata  domin  duba lafiyarsa  a kasar ta Jamus.

Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo,  Wole Ogunmolasuyi, wanda  ya  tabbatar da dawowar  gwamnan  ga wakilinmu, Ya ce  a yanzu haka  gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.

Kazalika maid akin  gwamnan,  Uwargida  Betty ta tabbatar da dawowar  mai gidan  nata  a shafinta na X, inda  ta wallafa hotonsa a  cikin jirgin sama.