On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Gwamnan Bankin Kasa Ya Yaudari Shugaban kasa Inji Adams Oshiomhole

Adams

To ba wai iya tsagin ‘yan hamaiyya ba ne suke irin wannan zargi, A yayin da shima jigo a cikin jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adam Oshiomhole,ya baiyana takaicinsa kan halin da matakin ya jefa al’ummar kasa.

Oshiohole ya  ce babban bankin kasa  CBN, Ya yaudari  shugaban kasa  muhammadu Buhari kan sauyin kudin da aka yi.

A  wata hira da aka yi  dashi a  gidan Talabijin na kasa  a karshen mako, Oshiomhole  ya nuna rashin amincewarsa  da daukar  matakin  ya mai  baiyana  shi a matsayin tsari na rashin  tunani da babban bankin kasa  yayi, domin wargaza  zabe mai zuwa.

Ya  kara  da cewa  tsabar  son zuciya  ce  tasa  babban bankin kasa  ya bullo  da tsarin.