On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnan Jihar Bayelsa Ya Umarci Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Su Koma Kananan Hukumominsu Da Zama

GWAMNAN JIHAR BAYELSA DOUYE DIRI

Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri Ya umarci daukacin zababban shugabannin Kananan Hukumomin jihar da aka rantsar su koma shalkwatar kanana hukumominsu da zama domin yin aiki yadda ya kamata.

Daukar matakin ya biyo bayan halin da mafi akasarin shugabannin kananan hukumomin jihar ke nunawa, inda suke komawa  Yenagoa babban birnin jihar da zama.

Da yake jawabi a wajen bukin rantsar da shugabannin Kananan Hukumomin   jihar, Gwamna Douye  Diri yace manufar  bijiro da tsarin  shine domin  ganin an samu cigaban da ake bukata a daukacin kananan hukumomin jihar.