On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnan Jihar Kano Abba Ya Karawa Sunusi Bature Matsayi Zuwa Darakta Janar Da Sauran Nade-Nade

Gwamna Abba Yusuf ya amince da daukaka matsayin mai magana da yawunsa, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, daga babban sakataren yada labarai zuwa  Darakta Janar na yada labarai.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na gidan gwamnatin jihar Kano, Aliyu Yusuf ya fitar cikin daren da ya gabata, ya ce nadin ya fara aiki nan take.

Sanarwar ta kuma bayyana nadin, wasu mukaman siyasa da suka hada da Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo, a matsayin Kwamishinan na 1 a hukumar Ilimin bai daya ta Kano   SUBEB da tshon mataimakin shugaban karamar hukumar Dala Hon. Surajo Imam Dala, a matsayin Darakta Janar na harkokin Kasuwanci.

Sauran sun hadar da Injiniya  Sarki Ahmad, Darakta Janar mai kula da hanyoyi da ayyukan a yankunan karkara da Dr. Dahiru Saleh Muhammad, Babban Sakataren zartaswa a hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha da Abubakar Adamu Rano, mataimakin shugaban gidan rediyon Kano sai Hajiya Hauwa Isah Ibrahim, Mataimakiyar Manajan  Darakta a gidan Talabijin na Abubakar Rimi da kuma Dr. Gaddafi Sani Shehu, Mataimakin Manajan Daraktan Kamfanin KHEDCO.